October 18, 2025

Yadda zargin luwaɗi da ƴan wasa ya janyo aka dakatar da koci na tsawon shekaru 20

images-2023-10-29T133505.548.jpeg

Muhammad Mahmud Aliyu

Rahotanni da suke fitowa daga hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya sun bayyana cewa ɓangaren shari’a na kwamitin ɗa’a na hukumar ya dakatar da Mista Jonathan Bukabakwa ɗan ƙasar Kwango daga duk wasu harkokin wasan ƙwallon ƙafa har na tsawon shekaru ashirin, tare da biyan tara da ta kai kimanin naira miliyan casa’in.

An samu mista Jonathan ne da laifin yin lalata da wani ɗan wasa mai ƙananan shekaru.

Shi dai mista Jonathan ya kasance tsohon mai horas da ‘yan wasa ne na ƙungiyar Urban Football Agreement, da ke buga wasanninta a yankunan Lipopo da Malebo a Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Kwango.

Wannan dakatarwa ta samo asali ne daga zarge-zarge da kafofin yaɗa labarai suka riƙa yi kan cin zarafin ‘yan wasa masu ƙananan shekaru da ke faruwa a Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta ƙasar Kwango (FECOFA).

Kuma an dangana mafi yawan zarge-zargen kan masu horas da ‘yan wasa, wanda hakan ne ya jawo aka dakatar da mista Jonathan na tsawon wata biyar a farkon wannan shekarar.

An yake wannan hukunci ne na dakatar da mista Jonathan bayan samun gamsassun hujjoji da suka bayyana cewa tabbas ya aikata laifn da ake zarginsa da aikatawa.

Tuni dai aka aika wa Mista Jonathan da takarda mai ɗauke da duk bayanan hukuncin da aka yanke masa a ranar ashirin ga wannan watan da muke ciki.

Hukumar ta FIFA ta bayyana cewa ba za lamunci duk wani nau’i na cin zarafi, nuna wariya ko kuma tsangwamar waɗanda suke ƙarƙashin koci ba.