Lamine Da Vinicius: Hansi Flick Ya Koka Kan Rashin Kariya Ga Taurarin ‘Yan Wasa a La Liga

Kocin Barcelona, Hansi Flick, ya bayyana damuwarsa kan yadda alƙalan wasa a gasar La Liga ba sa ba da kariya ga taurarin ‘yan wasa kamar na Barcelona da Real Madrid, lamarin da ke bai wa ‘yan wasan baya damar yin ƙeta ba tare da hukunci ba.
Flick ya yi kira ga alƙalan su kare lafiyar ‘yan wasa kamar Lamine Yamal na Barcelona da Vinicius Jr na Real Madrid ta hanyar ɗaukar mataki kan masu aikata mugun wasa. Ya ce dole ne a daina barin ‘yan wasan baya su riƙa cin zarafin ‘yan gaba yayin ƙwace ƙwallo ba tare da hukunci ba.
A ‘yan kwanakin nan, alƙalancin La Liga ya jawo cece-kuce, inda ƙungiyoyi kamar Real Madrid, Alaves, Real Sociedad, Rayo Vallecano, da Leganes suka bayyana rashin gamsuwarsu da ingancin alƙalanci.
Ko da yake Flick a baya ya nemi a ba da kariya ga alƙalan wasa, yanzu ya nuna damuwarsa kan yadda ake kula da lafiyar ‘yan wasa.
Rahotanni daga StatMuse sun nuna cewa Vinicius Jr da Lamine Yamal na daga cikin ‘yan wasan da aka fi yi wa ƙeta a La Liga, inda aka tafka wa Vini ƙeta sau 50, yayin da Yamal kuma aka yi masa sau 43.
“Muna bukatar a kare kowane ɗan wasa, ba wai kawai Lamine, Vini ko Raphinha ba,” in ji Flick, kamar yadda shafin Goal ya ruwaito. “Idan aka yi ƙwace ƙwallo da ganganci, dole a ba da yalon kati, idan ba haka ba, za a ci gaba da maimaita hakan. ‘Yan wasan baya na bukatar su fahimci cewa ba za a kyale su su yi ganganci ba.”
Flick, wanda ke jagorantar Barcelona a kakarsa ta farko, na samun sakamako mai kyau, inda kungiyar ke saman teburin La Liga, kuma a gasar Zakarun Turai suna cikin matakin zagayen ‘yan-16, inda za su kara da Benfica.