January 15, 2025

FIFA ta sa wa tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Spain Rubiales takunkumi na tsawon shekaru 3 saboda laifin sumbata

0
images-2023-10-30T172216.668.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA, ta sanar a ranar Litinin cewa ta dakatar da tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Spain, Luis Rubiales, daga duk wasu harkokin da suka shafi ƙwallon kafa a matakin kasa da kasa na tsawon shekaru uku.

Wannan mataki ya zo ne bayan da Rubiales ya sumbaci wacce ta lashe gasar cin kofin duniya Jenni Hermoso a lokacin bikin lambar yabo bayan da Spain ta lashe gasar cin kofin duniya ta mata a Sydney a watan Agusta.

Da farko FIFA ta dakatar da Rubiales na wucin gadi na tsawon kwanaki 90 sakamakon sumbata ba tare da neman izini ba.

A cikin wata sanarwa da FIFA ta fitar ta ce, “Kwamitin ladabtarwa na FIFA ya haramtawa Luis Rubiales, tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Spain (RFEF) shiga duk wasu harkokin da suka shafi kwallon kafa a matakin kasa da kasa har na tsawon shekaru uku.”

FIFA ta nanata kudurinta na mutuntawa da kare mutuncin kowane mutum, tare da tabbatar da cewa an kiyaye ka’idojin da suka dace.

An sanar da Rubiales game da hukuncin, kuma yana da kwanaki 10 don neman shawarar da za a yanke, wanda idan an buƙata, za a buga shi a shafin yanar gizon shari’a na FIFA.

Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa matakin na iya yiwuwa a daukaka kara a gaban kwamitin daukaka kara na FIFA.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *