An kama wasu da ake zargi da fasa rumbun ajiya da sace kayayyaki a Abuja
Daga Sabiu Abdullahi
Rundunar ‘yan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta ce ta kama wasu mutane 15 da ake zargi da hannu a barna a wani dakin ajiyar kaya na Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya da ke Abuja.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi a Abuja.
Ta ce wasu jami’an tsaro guda biyu da hukumar kula da ɗakunan na daga cikin wadanda ake zargin kuma aka kama kan barnar a dakin ajiyar da ke unguwar Tasha a Abuja.
Ms Adeh, wata Sufeta ta ce an kwato buhunan masara 26, Babura 5 da wasu kwanukan rufin Aluminium da aka lalata.
“Rundunar ‘yan sanda a Abuja ta samu cikakken bayani game da harin ba-zata da aka kai a kantin sayar da kayan abinci na Agric Department da ke unguwar Tasha a Abuja, a ranar 3 ga Maris.
“Rundunar tana so ta bayyana cewa tun daga lokacin, an saita al’amura a yankin,” in ji ta.