Sojojin Najeriya Sun Ceto Mutane 21 Da Aka Sace Ciki Har Da ‘Yan Kasar China 4
Sojojin rundunar Najeriya sun samu nasarar ceto mutane 21 da ‘yan bindiga suka sace a jihohin Kwara da Kogi, ciki har da ‘yan kasar Sin gida 4.
A wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai na rundunar, Laftanal Kolo Polycarp Okoye, ya fitar a ranar Asabar, ya ce an gudanar da aikin ceton ne ranar Alhamis, 17 ga Oktoba, 2025, karkashin shirin Operation FANSAN YAMA da ke yaki da ‘yan bindiga a yankin Arewa ta Tsakiya.
A cewar Okoye, aikin ya samu hadin gwiwar sojojin Brigade ta 12 da ke Lokoja da kuma Brigade ta 22 mai sulke da ke Ilorin. Ya ce wadanda aka ceto sun hada da maza 14, mata biyar, jariri daya, da kuma ‘yan kasar Sin guda 4.
Ya bayyana cewa wasu daga cikin mutanen da aka kubutar sun shafe fiye da watanni hudu a hannun masu garkuwa da su kafin a sake su.
Okoye ya kara da cewa an kai wadanda aka ceto asibitin sojoji domin samun kulawar farko da jinya, inda ya bayyana cewa “yawancinsu sun rame sosai saboda gajiya, amma yanzu suna murmurewa.”




