October 18, 2025

Sojojin Najeriya Sun Ceto Mutane 17 da Aka Sace a Kaduna

images - 2025-04-11T060501.455

Daga The Citizen Reports

Dakarun rundunar sojin Najeriya da ke karkashin atisayen Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutane 17 da masu garkuwa da mutane suka sace a Jihar Kaduna.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta bayyana cewa dakarun Sashen 1 ne suka gudanar da wannan aiki mai cike da nasara.

Mutanen da aka kubutar sun hada da Samuel Ezekiel, Williams Ezekiel, Duza Ezekiel, Ishaku Ezekiel, Sunday Ezekiel, Alice Ezekiel, Victoria Ezekiel, Favor Ezekiel, Rebecca Obadiah da Blessing Obadiah.

Sauran sun hada da Alheri Obadiah, Gift Obadiah, Jummai Obadiah, Gloria Obadiah, Charity Obadiah, Friday Jessy da Theresa Friday.

Bayan an ceto su, sojojin sun tabbatar da cewa an duba lafiyar wadanda aka ceto, tare da yin musu cikakken bayani da daukar bayanansu kafin a mika su ga rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kaduna a ranar da aka ceto su domin mayar da su cikin gaggawa ga iyalansu.