April 19, 2025

Sanata Ali Ndume Ya Caccaki Shugaba Tinubu

0
Muhammad8

Sanata Ali Ndume, mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu a majalisar dokoki ta kasa, ya yi kaca-kaca da yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke nada mukaman siyasa tun bayan hawansa mulki.

Ndume ya bayyana cewa nade-naden suna sabawa tanadin kundin tsarin mulki, musamman sashen da ya shafi wakilcin kowane yanki na kasar nan (federal character).

A wata hira da aka yi da shi a tashar Arise TV, Sanatan ya zargi shugaban kasa da fifita yankin da ya fito, wato Kudu maso Yamma, wajen nade-nade.

Ya ce rashin daidaito da bambancin yankuna a cikin nade-naden yana sabawa tanadin Sashe na 14 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *