June 14, 2025

APC Ta Amince da Ganduje Ya Cigaba Da Zama Shugabanta

images-2025-02-26T190025.359.jpeg

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta amince da ci gaba da jagorancin shugabanta na riƙo, Abdullahi Umar Ganduje.

A taron da jam’iyyar ta gudanar yau Laraba a Abuja, manyan jiga-jiganta sun bayyana gamsuwa da irin rawar da Ganduje ke takawa tun bayan naɗa shi a watan Agustan 2023.

Wannan mataki na nufin tsohon gwamnan Kano zai ci gaba da jan ragamar jam’iyyar har zuwa babban taron ƙasa na APC, wanda za a gudanar domin zaɓen cikakken shugaba.

Ganduje ya zama shugaban jam’iyyar na riƙo ne bayan da kwamitin gudanarwa na APC ya tabbatar da shi a watan Agustan 2023, bayan murabus ɗin tsohon shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu.