April 18, 2025

Atiku Abubakar Ya Kai Ziyarar Gaisuwar Sallah Ga Muhammadu Buhari

0
FB_IMG_1744384191525

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya kai ziyarar gaisuwar Sallah ga tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a gidansa da ke Kaduna.

Tare da Atiku a ziyarar akwai tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai; tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal; da wasu fitattun jiga-jigan siyasa.Atiku ya wallafa bidiyo daga ziyarar a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana cewa sun kai gaisuwa kuma sun yi dariya sosai da tsohon shugaban.

Ya ce: “A matsayina na Wazirin Adamawa, na tsaya domin gudanar da shagulgulan Sallah a Adamawa, inda na wakilci Sarkin Adamawa, Lamiɗo Fombina. Yau kuma na kai ziyarar gaisuwar Sallah ga Muhammadu Buhari… kamar yadda ya saba, ya yi ta ba mu dariya har haƙarƙarina suka yi zafi.”

Sai dai Atiku bai bayyana ko sun tattauna wani batu da ya shafi siyasa ba a lokacin ziyarar.

Ziyarar na zuwa ne a wani lokaci da ake ta samun yawaitar ziyarar siyasa daga manyan jami’an gwamnati da ƴan siyasa zuwa wajen tsohon shugaban tun bayan dawowarsa daga Daura zuwa Kaduna bayan sauka daga mulki.

Ziyarar El-Rufai a baya-bayan nan zuwa wajen Buhari ita ce ta fi ɗaukar hankalin jama’a, duba da yadda jim kaɗan bayan hakan ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa SDP — wata alama da wasu ke fassara a matsayin sauyin salo a siyasar Najeriya gabanin babban zaɓen ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *