February 10, 2025

Firaministan Lebanon Ya Yi Tattauna Kan Tsaron Iyakokinsu Da Syria

3
image_editor_output_image800240022-1736667232055.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Firaministan Lebanon, Najib Mikati, ya bayyana cewa Lebanon da Syria za su yi aiki tare don tabbatar da tsaron iyakokin kasashen biyu. Mikati ya yi wannan bayani ne yayin taron manema labarai da ya gudanar tare da sabon shugaban Syria, Ahmed al-Sharaa, a birnin Damascus.

Wannan ziyara ce ta farko a hukumance da wani shugaban Lebanon ya kai Syria tun bayan barkewar yaƙin basasar kasar a shekarar 2011.

Duk da haka, a kwanakin baya, dangantaka tsakanin kasashen biyu ta sake yin tsami, inda a makon da ya gabata Syria ta sanya sabbin takunkumi kan shigar ƴan Lebanon zuwa kasarta. Wannan mataki ya biyo bayan tarzoma ce da ta taso a kan iyakar kasashen biyu.

Har ila yau, kungiyar Hezbollah, wadda ke da hedkwata a Lebanon, ta kasance cikin masu goyon bayan gwamnatin Bashar al-Assad yayin daƙon yaƙin basasar Syria.

Wannan taron na alamta sabon yunƙuri na farfado da alakar diplomasiyya tsakanin Lebanon da Syria bayan shekaru da dama na rashin jituwa.

3 thoughts on “Firaministan Lebanon Ya Yi Tattauna Kan Tsaron Iyakokinsu Da Syria

  1. Hi, I doo believe thgis iss aan excellednt blog. I stumbledupon it 😉 I’m ggoing tto ccome bazck once agan siknce I book-marked it.

    Monery andd freddom iis tthe greattest wway too change, mayy you be rih and contginue tto guide other people.

  2. Doess your website have a contacct page? I’m having problems locating
    it but,I’d luke to send you aan email. I’ve gott some suggestionhs foor your blpg you might be interestedd inn hearing.
    Either way, great website aand I look forwardd tto seeing iit expad ovver time.

  3. Hi there, Youu have one a fantwstic job. I’ll definitely diggg
    iit aand pesrsonally suggest tto my friends. I’m confident they’ll bee benefited froom this weeb site.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *