Yadda Wani Laccara Ke Fafutukar Yaƙar Cutar Sikila Da Wayar Da Kai Kan Gwajin Genotype Kafin Aure

Daga: Kasim Isa Muhammad
Fassara: Sabiu Abdullahi
Aliyu Bakama malami ne a Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Jihar Gombe, kuma yana fama da cutar sikila (watau sickle cell a Turance). Bugu da ƙari, shi ne wanda ya kafa ƙungiyar A5 Sickle Cell Initiative a Jihar Yobe. An haife shi a garin Potiskum, kuma ya sadaukar da rayuwarsa wajen yaki da yawaitar cutar sickle cell.
Ta hanyar wannan ƙungiya, Aliyu ya samar da hanyoyin wayar da kai, ya yi fafutuka domin tabbatar da gwajin genotype kafin aure, kuma yana tallafa wa masu fama da wannan cuta. A wannan tattaunawa da TCR (The Citizen Reports), Aliyu ya bayyana irin ƙalubalen da ya fuskanta, dalilin kafa wannan ƙungiya, da kuma nasarorin da ya samu.
TCR: Za ka iya bayyana mana yadda kake ji a rayuwa da kake ɗauke da cutar sickle cell?
Aliyu: Rayuwa da cutar sikila ba abu ne mai sauƙi ba. Raɗaɗin ciwon yana da tsanani matuƙa—ba wanda bmzai iya misalta shi sai dai wanda ke ɗauke da ita. Duk da haka, cutar ba ta hana ni cimma burina ba. A yau, ni Malami ne (Lecturer III) a Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Gombe. Wannan nasara ta nuna cewa da jajircewa da azama, mutum zai iya cimma burinsa, duk da kowane irin hali.
A lokacin da nake ƙuruciya, na fuskanci cin zarafi da raini daga abokan makaranta saboda ƙarancin tsawo na da rashin lafiya a-kai-a-kai. Suna kirana da suna “Smally,” duk da cewa shekarunmu ɗaya ko ma na girme su. Amma iyayena sun ba ni ƙarfin gwiwa, suka kuma taimake ni har na tsallake waɗannan matsaloli.
TCR: Yaya cutar ta shafi shawararka ta kafa ƙungiyar A5 Sickle Cell Initiative?
Aliyu: Ganin yadda na tsinci kaina da wannan cuta ya koya min alherai da muhimmancin daukar matakin rage yaduwarta. Wannan shi ne dalilin kafa A5 Sickle Cell Initiative, domin wayar da kai kan cutar sickle cell da kuma tilasta gwajin genotype kafin aure.
Ba ni kaɗai nake wannan kokari ba. Na haɗa kai da abokan aiki kamar Muhammad Yalwe da Yakubu Salisu, muka tattara tunani da albarkatunmu don kafa wannan ƙungiya.
TCR: Wanne irin ƙalubale ka fuskanta yayin tafiyar da wannan ƙungiya?
Aliyu: Ƙalubalen suna da yawa. Babbar matsala ita ce rashin isasshen kuɗi domin tallafa wa marasa lafiya. Duk da cewa muna samun gudunmuwa daga mutane masu kirki, ba ya wadatarwa.
A matsayina na mai fama da cutar, na fuskanci matsaloli masu yawa tun daga ƙuruciya. Rashin lafiya a-kai-a-kai yana hana ni zuwa makaranta, kuma hakan ya sa wasu ke raina ni. Amma na dage, kuma na kasance mai hakuri da jajircewa.
TCR: Me ya ba ka kwarin gwiwar kafa wannan ƙungiya, kuma mene ne manufarta?
Aliyu: Ƙirƙirar wannan ƙungiya ya samo asali ne daga abin da na fuskanta da ciwon sickle cell. Na san irin wahalhalun da masu fama da wannan cuta ke sha, kuma na so in zama muryarsu.
Manufarmu ita ce:
-Wayar da kai da tilasta gwajin genotype kafin aure.
-Shirya bitoci da tarurrukan ilmantarwa.
-Ba da shawarwari ga marasa lafiya da iyalansu.
-Samar da dakin bincike kan cutar sickle cell.
TCR: Wadanne shirye-shirye A5 Sickle Cell Initiative ke gudanarwa?
Aliyu: Muna gudanar da shirye-shirye kamar:
-Yin gangamin wayar da kai: Muna shirya taruka da makon sanin cutar sickle cell, inda muke tattauna illolinta da hanyoyin kariya.
-Shirin tallafa wa marasa lafiya: Muna biya wa yara 20 masu fama da sickle cell kudin makaranta.
-Tallafin jinya: Muna biyan kudin magani ga marasa lafiya da ba za su iya biya ba.
-Shirin koyar da sana’o’i: Muna koyar da sana’o’in zamani kamar amfani da kwamfuta da haɗa turare.
A kwanan nan, mun samu tallafin inshorar lafiya ga masu fama da cutar a Potiskum ta hannun Basic Health Care Programme Fund.
–TCR: Wadanne matsaloli kuka fuskanta a tafiyar da wannan ƙungiya?
Aliyu: Babban ƙalubalen da muka fuskanta shi ne rashin karɓuwa daga wasu al’umma. Wasu sun yi tunanin muna kokarin kawo wani sabon salo da ba ya dacewa da al’ada ne. Amma muka cigaba da wayar da kai har suka fahimta.
Haka nan, ba mu samu tallafi daga gwamnatin Jihar Yobe ba, duk da irin ƙoƙarin da muke yi. Wannan ya samo asali ne daga tsarin da ke fifita ‘yan uwa da abokai a maimakon cancanta. Amma ba za mu karaya ba.
TCR: Wadanne nasarori kuka cimma?
Aliyu: Daya daga cikin manyan nasarorinmu shi ne samun zama memba a cikin Global Action Network for Sickle Cell and other Inherited Blood Disorders (GANSID) da ke Amurka, wanda aka samu ta hanyar kokarin Mr. Lanre Tunji-Ajayi.
TCR: Me kuke fatan cimma a nan gaba?
Aliyu: Muna fatan kawo cigaba ta hanyar ƙaddamar da ƙungiyarmu a matakin duniya, domin inganta bincike da goyon bayan masu fama da cutar sickle cell. Muna kokarin haɗa kai da manyan ƙungiyoyi na duniya domin cimma wannan buri.
TCR: Ta yaya mutane da al’umma za su iya tallafa wa wannan ƙungiya?
Aliyu: Ana iya tallafa mana ta hanyoyi da dama. Mutane na iya bada taimako ta jiki da ilimi, ko taimakawa wajen yaɗa ilimi game da cutar sickle cell.
Har ila yau, tallafi na kudi yana da matukar muhimmanci domin taimaka wa masu bukata. Ga duk wanda yake sha’awar ba da gudunmuwa, yana iya tuntuɓar mu ta shafukan sada zumunta. Facebook dina shi ne Aliyu Bakama.


l9hno3
Hi there it’s me, I aam alkso visiting thi web
page on a rdgular basis, ths sire is rrally nice and tthe viewers aree actualoly
suaring good thoughts.