October 18, 2025

Masarautar Bauchi ta tuɓe masu sarautu guda shida

images-2023-11-11T095631.937.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Masarautar Bauchi ta dauki matakin da ba a taba ganin irinsa ba na korar wasu masu riƙe da sarautar gargajiya guda shida a yankin Galambi.

Matakin na zuwa ne a sakamakon rashin gamsuwar da masarautar game da yadda ake tafiyar da naɗin sarauta, saboda rashin bin ka’idojin da aka kafa.

Idan ba a manta ba, Hakimin Galambi Alh. Shehu Adamu Jumba, da Danlawal na Masarautar Bauchi, sun ɗauki nauyin naɗa sarakunan gargajiya da suka haɗa da Galadiman Danlawal, Majidadin Danlawal, Wakilin Dokan Danlawal, Wakilin Gonan Danlawal, Sarkin Dajin Danlawal, da Hardon Danlawal.

Sai dai wannan matakin bai samu amincewar Majalisar Masarautar ba, lamarin da ya sa aka cire su daga muƙamansu daga baya.

Babban jami’in yaɗa labarai na Masarautar Bauchi Malam Babangida Hassan Jahun ne ya bayyana hakan a zaman da majalisar ta yi a kwanakin baya.

17 thoughts on “Masarautar Bauchi ta tuɓe masu sarautu guda shida

Comments are closed.