December 7, 2025

Daukan Hukunci A Hannu: Ni ma Da Kyar Na Sha a 1973

image_editor_output_image-1945569043-1699184597054.jpg

Daga Dr. Aliyu U. Tilde

Wannan hoton wani yaro ne wanda na gani a post din Musa Madaki yanzu. Wani yaro ne da shanunsa suka yi karamar barna a gonar wani manomi a Jahar Naija, kamar yadda Malam Musa ya ba da labari. Manomin ya dau doka a hannunsa ya datse hannuwan yaron, ya kuma sare wuyansa.



Kash, sai kuma aka gane yaron ba danfulani ba ne, gaynaako ne, watau dan wata kabilar ne aka yi jinga da shi ne ya yi kiwo don iyayensa su sami na abinci.

Daukan doka a hannu kullum karshensa nadama. Abubuwa a duniya da yawa ba kamar yadda muke daukan su ba ne da farko. Shi ya sa bincike yake da amfani don tabbatar da laifi kafin a dauki hukunci.

Na tuna a shekakar 1973 ina kiwo a hanyar Kogin Kalwa, haka kawai sai wani tsoho Bajarin duste ya zo ya ce na mar barna, alhali kuwa sam ba abinda ya taba gonarsa. Sai ya juya ya je gida ya dauko baka da kwari zai harbe ni. Allah ya sa mahaifina da sauran yan zawiyyar marigayi Malam Baba suna yanke dawar Malam din a gonarsa da ke gefe, wacce nake jira in ci karanta in sun kare yanka. Sai na je gunsa na ce ga wani Bajari zai harbe ni siddan. Sai ya daka mun tsawa, ya ce me ya sa zan bar shanu, in je ya harbe ni din. Sauran dattijai suka ce, Alhaji a je a duba. Sai ya karbi sandata ya doshi Bajarin. Ganin mahaifina sai Bajarin ya ja da baya, yana cewa bai ce zai harbe ni ba, ya koma gida. Da haka na sha… 😀

Daya daga cikin abubuwan da muka gano yake yawaita barna shi ne sa kananan yara kiwo wadanda akasari ma ba yanfulani ba ne. Zai yi kyau hukuma ta sa doka kan duk wanda zai yi kiwo ya zame baligi. Wannan zai takaita barna da ake samu idan shanu sun gagari yaro makiyayi.

Haka matsalar makiyaya da manoma take tun fil azal. Hukuma ko sarakuna ko masu gari ke warware ta ta hanyar diyya. Amma daukan mataki a hannu ba abinda zai haifar sai nadama. Haka yake duk duniya. Kuma da yake manoman da makiyayan sau da yawa daga jinsuna mabambamta suke, a take sai abin ya dau salon kabilanci.

Ni dai na sha da kyar shekaru hamsin da suka wuce. Amma wannan yaron na Naija an cuce shi har abada. Allah sa mu fi karfin zuciyarmu.