January 14, 2025

Ƴan sanda sun kama waɗanda ake zargi da kashe Nafiu Hafiz

0
image_editor_output_image-2123633045-1703272676402.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Ƴan sandan Jihar Kano sun kama wata matar aure ƴar shekaru 24 mai suna Hafsat Surajo da laifin daɓa wa wani matashi mai suna Nafi’u Hafiz wuka har lahira.

Rundunar ‘yan sandan ta ce lamarin ya faru ne a Unguwa Uku da ke karamar hukumar Taurani a jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hussaini Gumel, ne ya tabbatar da hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Juma’a.

Ya ce a ranar 21 ga watan Disamba da misalin karfe 0700 ne aka samu rahoto daga wani Hafizu Salisu na karamar hukumar Bauchi, cewa wani Daiyanu Abdullahi a Unguwa Uku Kano ya kira shi a waya cewa dan uwansa Nafi’u Hafiz ya mutu.

Ya bayyana cewa, a lokacin da dan’uwan ya isa gidan da abin ya faru a Unguwa Uku, sun ga raunuka da dama a sassa daban-daban na mamacin da ake zargin da wuƙa aka yi masa.

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce bincike ya kai ga kama wadanda ake zargin, Hafsat Surajo, wacce wata matar aure ce a gidan da mamacin ke zaune.

Ya ƙara da cewa wacce ake zargin ta amsa aikata laifin.

“An kama mijinta mai suna Dayyabu Abdullahi da kuma mai gidansu Malam Adamu da laifin taimakawa, tattara kaya da kuma boye gawar domin su rufa-rufa game da kisan gillar,” inji shi.

Ya kara da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *