Gwamnan Kogi Yahaya Bello ya tsallake rijiya da baya
A yau Lahadi ne gwamnatin jihar Kogi ta bayyana cewa an yi yunƙurin kashe gwamnan jihar Yahaya Bello a kusa da Abuja a kan hanyarsa ta zuwa wani aiki daga Lokoja, babban birnin jihar.
A cewar wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kingsley Fanwo ya fitar, ta bayyana cewa harin ya afku ne da misalin karfe 4 na yamma a ranar Lahadi, 22 ga Oktoba, 2023.
A cewarsa, “Maharan wadanda suke sanye da kakin soji sun yi wa ayarin motocin gwamnan wuta, inda suka fara harbe-harbe kan motarsa da sauran motocin da ke cikin ayarin. Sai da jami’an tsaron da ke tare da gwamnan suka yi gaggawar shiga tsakani don daƙile shirin na mutanen da ba a san ko su waye ba.”
Ya ce an kai hare-haren ne a wurare uku daban-daban, inda shingayen karshe ya kasance na daura ne da babban birnin tarayya, Kwali, da misalin karfe 4.20 na rana.
Ya yi kira ga jama’a da su kasance masu lura da kuma kai rahoton duk wani yunƙuri da ba a yarda da shi ba ga jami’an tsaro.