Tinubu ya tabbatar wa masu zuba jari na Saudiyya cewa za su ci riba idan suka so Najeriya
Daga Sabiu Abdullahi
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu a ranar Juma’a ya buƙaci masu saka hannun jari a Saudiyya da su je Nijeriya domin zuba jarinsu saboda za su ci riba.
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ake gudanar da taron Kasashen Afirka da Saudiyya a babban birnin kasar, watau Riyadh.
An ambato shugaban yana cewa, “Ina tabbatar wa ’yan Saudiyya masu saka hannun jari cewa za a kare dukiyarsu bisa doka, kuma za su ci riba a ƙasar da ta fi ƙarfin tattalin arziki a Afirka. Don haka, buɗe hukumar da za ta kula da kasuwanci tsakanin Nijeriya da Saudiyya na da matuƙar muhimmanci.”