October 18, 2025

Kotun ɗaukaka ƙara ta soke hukuncin da ya tuɓe Gwamna Sule na Nasarawa daga kujerarsa

images-2023-11-23T115759.568.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke tsige gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, inda ta mayar da shi a matsayin zababben gwamnan da ya ci zaben gwamnan da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.

A wani mataki na bai-daya da alkalai uku suka yanke a ranar Alhamis, sun bayyana cewa hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta jihar Nasarawa ta yanke tun da farko an soke shi.

Hakan na nufin kotun daukaka karar ta yi watsi da hukuncin da kotun ta yanke na tsige Gwamna Sule.

Wannan al’amari na shari’ar ya zo ne bayan wani cikakken nazari da kotun daukaka karar ta yi, inda ta tabbatar da cewa hukuncin da waccar kotun ta yi akwai kura-kurai a cikinsa.

13 thoughts on “Kotun ɗaukaka ƙara ta soke hukuncin da ya tuɓe Gwamna Sule na Nasarawa daga kujerarsa

Comments are closed.