Lalong zai sauka daga mukaminsa na minista don komawa sanata
Daga Sabiu Abdullahi
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong, ya karbi takardar shaidar cin zabe a hukumance a matsayin Sanata mai wakiltar Filato ta Kudu.
An gabatar masa da takardar shaidar ne a Abuja, babban birnin kasar a ranar Alhamis.
Wannan lamari ya biyo bayan kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin kotun da ta bayyana Lalong a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Filato ta Kudu.
Kwamitin mai mutane uku karkashin jagorancin Elfrieda Williams-Dawodu, ya tabbatar da hukuncin kotun, inda ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta kasa bin umarnin kotu na gudanar da wani sabon taro a kananan hukumomi 17 na jihar.
A yanzu da ya samu takardar shedar dawowarsa, ana sa ran cewa Lalong zai yi murabus daga mukaminsa na minista domin kaddamar da shi a matsayin Sanata a majalisar dattawa.