January 14, 2025

Shahararren farfesa a Najeriya Ezzeldin Muktar Abdurrahman ya rasu

3
FB_IMG_1700755304751.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

A yau ne aka yi jana’izar Farfesa Ezzeldin Muktar Abdurrahman, fitaccen malami kuma tsohon shugaban Jami’ar Jihar Bauchi, da misalin karfe 4:00 na yamma a Zaria da ke Jihar Kaduna.


An haife shi a ranar 18 ga Nuwamba, 1957, a Masar.


Ya sami digirin digirgir na kimiyyar harhada magunguna daga Jami’ar Alƙahira a shekarar 1980.


Ya ci gaba da neman ilimi, inda ya samu digiri na biyu a 1986, da digiri na uku a 1998, da kuma mastas a harkar kasuwanci (watau MBA) a 1999.

Farfesa Abdurrahman ya yi jagoranci a matsayin Shugaban Sashen kuma Shugaban Kimiyyar Magunguna a ABU.


Aikin jagorancinsa ya kai ga ya zama shugaba aJami’ar Jihar Kaduna da Jami’ar Jihar Bauchi.

3 thoughts on “Shahararren farfesa a Najeriya Ezzeldin Muktar Abdurrahman ya rasu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *