January 15, 2025

Kotu ta tabbatar da zaben gwamnan Kebbi Nasir Idris

11
Nasir-Idris.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da zaben gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, a matsayin halattaccen gwamnan jihar.

Kotun ta yi watsi da karar da PDP da dan takararta na gwamna mai ritaya, Maj.-Gen. Aminu Bande, ya suka shigar, kuma ta ayyana Dr Nasir Idris na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin zababben gwamnan jihar Kebbi.

Kwamitin mutum uku na kotun karkashin mai shari’a Ofem Ofem ya yi watsi da karar da Manjo Janar Aminu Bande (mai ritaya) na jam’iyyar PDP ya shigar kan rashin cancantar ƙarar.

Kotun ta ce wanda ya shigar da karar ba zai iya tabbatar da zargin da suke yi na takardun jabu ba, tare da rashin bin ka’idojin dokar zabe.

11 thoughts on “Kotu ta tabbatar da zaben gwamnan Kebbi Nasir Idris

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *