June 14, 2025

Reno Omokri Ya Caccaki El-Rufai Kan Suka da Ya Yi wa Dokar Ta-Baci a Jihar Rivers

Tsohon mai ba wa shugaban kasa shawara, Reno Omokri, ya caccaki tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, bisa kalaman da ya yi na sukar dokar ta-baci da aka kafa a Jihar Rivers.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X (wanda a da ake kira Twitter), Omokri ya zargi El-Rufai da kokarin tunzura al’umma su ki gwamnatin tarayya. Ya kuma jaddada cewa duk da sukar da El-Rufai ke yi, dansa, Bello El-Rufai, wanda ke majalisar wakilai, bai tsaya don kalubalantar dokar a majalisa ba.

Omokri ya yi wa tsohon gwamnan ba’a, yana mai cewa El-Rufai na kokarin tunzura ‘yan Najeriya a dandalin sada zumunta, amma bai bari ‘ya’yansa su shiga cikin batun ba.

“Ba zai iya sa dansa ya yi wannan aiki ba, sai dai shi ya zo nan yanar gizo yana tunzura ku, saboda rayuwarku da makomarku ba su kai masa matsayin rayuwar dansa da makomarsa ba,” in ji Omokri.

Maganganun na zuwa ne a daidai lokacin da ake tafka muhawara mai zafi kan rikicin Jihar Rivers, inda bangarori daban-daban ke kalubalantar doka da hujjojin da suka sa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kafa dokar ta-baci a jihar.