Buhari Ya Tattara Ya Koma Kaduna Da Zama Bayan Shafe Lokaci a Daura

Tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya koma gidansa da ke Kaduna bayan ya shafe lokaci a mahaifarsa, Daura, jihar Katsina, tun bayan saukarsa daga mulki a Mayun 2023.
Bashir Ahmad, tsohon mai taimaka masa na musamman, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa Buhari ya samu rakiyar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, Gwamnan Borno, Babagana Zulum, da Gwamnan Kaduna, Uba Sani.
Haka nan, wasu ‘yan siyasa da tsofaffin jami’an gwamnati sun tarɓi tsohon shugaban kasa a gidansa da ke Kaduna.