Harin bam: Kashim Shettima ya tafi ta’aziyya Kaduna
Daga Sabiu Abdullahi
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya isa jihar Kaduna domin jajanta wa yan uwan mutanen da kuma iyalan wadanda suka mutu a harin da a kai makon da ya gabata.
Harin da sojojin suka kai a ranar Lahadin da ta gabata ya faru ne a kauyen Tudun Biri da ke cikin karamar hukumar Igabi a jihar, inda ake kyautata zaton an kashe mutane sama da 100.
Kashim ya samu tarbe a sansanin sojin saman Najeriya da ke Mando.
Gwamna Uba Sani da manyan jami’an gwamnatin jihar Kaduna ne suka tarbe shi.
Mataimakin shugaban kasar ya samu rakiyar ministan tsaro Abubakar Badaru; Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje; Kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbass.
Tun da farko dai Shettima ya nufaci yin ziyara wa al’ummar da abin ya shafa a ranar Laraba amma ya yanke shawarar mayar da ziyarar tasa zuwa Alhamis.