January 15, 2025

Kashim Shettima ya tafi China don wakiltar Tinubu

0
FB_IMG_1697377893821.jpg

Suleiman Mohammed B.

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya tafi birnin Beijing na China don wakiltar Shugaba Bola Tinubu a wani taro.

Mista Stanley Nkwocha, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa (Ofishin Mataimakin Shugaban kasa) ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Lahadi.

Ya ce Shettima zai bi sahun shugabannin kasashen duniya sama da 130 na kasashen Afirka, Asiya, Turai da kuma Latin Amurka don yin shawarwari kan taken, “Hadin gwiwa mai inganci don ci gaba da samun wadatuwa.”

Ana sa ran ziyarar mataimakin shugaban kasar za ta amfani Najeriya bisa samar da tsari da dandali don jawo hankalin masu zuba jari don samun karin ayyukan raya kasa.

Shettima zai gana da wasu shugabannin kasashen duniya domin inganta huldar kasuwanci da zuba jari a Najeriya bisa tsarin bunkasa tattalin arzikin gwamnatin Tinubu.

Gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin za ta yi taro don bikin murnar alamar cika shekaru goma na Belt and Road initiative (BRI) wadda shugaban ƙasar China ya kaddamar da ita a shekarar 2013.

Shirin na neman daukar matakin kasa da kasa don inganta hadin gwiwa, da inganta zuba jarin samar da ababen more rayuwa a kasashe kusan 70 na Asiya da Afirka da Turai ta hanyoyin kasa da teku.”

Mai taimaka wa shugaban kasar ya tuna cewa a shekarar 2018, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da kasar Sin a madadin Najeriya.

Nkwocha ya bayyana cewa tawagar mataimakin shugaban kasar zuwa taron sun hada da ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Atiku Bagudu, da kuma ministan sufuri, Sa’idu Alkali.

Sauran sun hada da ministan ayyuka, David Umahi, ministan masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Dr Doris Uzoka-Anite; Babban Daraktan Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya, Fidet Okhiria, da Darakta Janar na Hukumar Kula da Rarraba Wutar Lantarki, Michael Ohiani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *