CBN ya dawo bayar da canjin dala ga masu shigo da kayayyaki 43 wadda gwamnatin Buhari ta hana
Daga Sabiu Abdullahi
Babban Bankin Najeriya CBN ya sanar da janye haramcin bayar da canjin dala don shigo da shinkafa, siminti da wasu kayyaki 41 cikin Najeriya.
Wannan yana ƙunshe ne cikin sata sanarwa da babban bankin ya fitar ranar Alhamis, ɗauke da sa hannun babban daraktan sadarwa, Isa AbdulMumin.
Hakan wani yunƙuri na taimaka wa kasuwar musayar kudade.
Idan ba a manta ba, a shekarar 2015 ne CBN ya taƙaita bayar da dala domin shigar da wasu abubuwa ƙasar, yana mai cewa bai su kamata a bayar da dala domin shigar da su ba, saboda a cewar gwamnati kayayyaki ne da za sa iya samu a cikin Najeriya.
Bankin ya ƙara da cewa a yanzu masu shigo da kayayyaki 43 ɗin nan za su iya samun canjin dala daga babban bankin.