October 18, 2025

Ajami a Sauƙaƙe, daga Abdalla Uba Adamu

FB_IMG_1715661208135.jpg

Daga Farfesa Abdalla Uba Adamu

Ba fitacce bane. Ban jin da yawa sun san shi, illa waɗanda yake mu’amala da su. Ni kai na ban san shi ba sai ta hanyar sadarwar zamani lokacin da ya lalubo ne domin sanar da irin yunƙurin da yake yi wanda ya yi daidai da nawa. Hasali, tun da na fara wannan yunƙurin, babu wanda ya taɓa nuna sha’awar karɓa daga waje na domin ci gaba da shi, sai yanzu. Kuma yunƙurin sa ya wuce nawa fiye da misali. Idan za a ce ni ne na ƙyasta ashanar yunƙurin, to shi ya ruruta wutar.

Sunan sa Abdullahi Abba Ɗalhatu. A yanzu ya na ƙasar Brazil yana digiri na uku a fannin fasaha da ƙere-ƙere a University of São Paulo. Yau shekara guda kenan (dalilin wannan rubutun) da fara magana da shi, wanda shi ya fara turo min da bayanin gabatarwa da kuma abin da yake tafe da shi. Ban taɓa haɗuwa da abin da ya birge ni a ƴan shekarun nan, kamar abin da Abdullahi ya ke yi ba. Ya gama faranta min a rayuwar boko, domin ya karɓi fitilar da nake ƙoƙarin haskawa, ya ƙara haskenta – da kuɗin sa, gumin sa, lokacin sa, basirar sa, kuma, kamar ni, ba a  fannin sa – fiye da yadda nake zato. Alhamdulillah. Ga tushen.

Tun 1996, a lokacin ina Tsangayar Ilimi ta Jami’ar Bayero (Faculty of Education) na ke da tunanin yadda za a canja aƙalar ilimintar da Almajirain tsangayu a ƙasar Hausa. Waɗanda suka san ni da jimawa, sun da da wannan. Na yi mu’amala da ƙungiyoyi sa kai da dama a kan wannan, taƙamaimai Amurkawa ta USAID. Kullum damuwar ita ce “akwai yara fiye da miliyar shida wadanda ba sa zuwa makaranta a Arewacin Najeriya.” A duk lokacin da ake wannan maganar, ana maganar ‘Almajirai’ ne. Kullum a matsayin jahilai ake ganin su saboda ba sa makarantun boko. Kuma tun kafin akai ga matsalar tsaro, jaridun mutanen kudancin Najeriya suka dodontar da Almajirai da nuni da cewa ai daga cikin su ne a ke samun ƴan boko haram. Sai da rigingimun ta’addanci suka yi tsamari sannan aka juya akalar rashin zaman lafiya daga Almajirai zuwa makiyaya.

Babbar manufata a wancan lokacin (kuma har yanzu), ita ce gusar da tunanin cewa duk Almajiri  jahili ne saboda bai yi karatun boko ba. Yaron da zai ɗauki Ƙur’ani mai tsarki wanda babu wani littafi kamar sa a duk halitta, ya rubuce shi, ya karance shi, sannan in hali ya yi, ya haddace shi, sannan a kira shi jahili? Tabbas masu cewa Almajirai jahilai ne, SU ne jahilan, saboda ba su san cewa tun 1349 aka  kafa tushen ilimin Almajarai a ƙasar Hausa ba. A lokacin mutanen su zigidir suke yawo a daji, ba gidaje, ba birane, ba kasuwanni, ba cinikayya, sai ka ce dabbobi.

Ƙalubalen shi ne, ta ƙaƙa za a juyar da akalar ilimi da basirar da Allah Ya bawa Almajirai ta yadda za ta dace da zamani? Amsa ta ita ce, “Ajamancin Ilimi” (Ajamization of Knowledge). Da na fara tuntuɓar mutane a kan wannan maudu’in, dariya waɗan su suka yi – domin ba su ga dangantakar Ajami da ilimi ba. Wani ma – wanda ya zama babban mutum daga baya – cewa ya yi da ni “yo kai da ka dame mu da wani Ajami, meye amfanin sa?” Kaɗan ne suka hango inda na nufa, kamar su Fatuhu Mustapha da Nasiru Wada Khalil, waɗanda suka zama malamai na a fannin saboda tari da zurfin ilimin da suke da shi.

Kai, har a wani gagarumin taro a Arewa House da aka yi a Maris 2003 tare manyan shehunanan malamai na lokacin na yi kokarin jawo hankali a kan abun, aka banzantar da ni. Na jawo hankali da rubutun da John Philips ya yi, mai suna “Spurious Arabic: Hausa and Colonial Nigeria”, amma ko a jikin su. Philips ya nuna muhimmacin Ajami a tarihin ƙasar Hausa. Ganin yadda aka banzantar da maganar – daga Malaman jami’a, zuwa Malaman addini da kuma jami’an gwamnati – sai na fara  tunanin ko ni ne na yi batan hanya ne? Koma in haƙura ne?

Wata rana yawon neman kuɗin Laraba ya kai ni Akwanga, a jihar Nasarawa. Na tsaya a wani gidan mai a wajen gari domin shan man mota. Bayan mai zubawar ya gama, na biya shi. Zan shiga motar kenan, sai na ga yana rubuta lissafin cinikin da aka yi a lokacin a wani littafin rubutu. Na tsaya ina gani, sai na lura da Ajami ya ke rubutawa. Na rufe motar na hau tattaunawa da shi. Ya nuna min sauran abubuwan – rubutu, saƙonni, d.s. –duk da Ajami yake yi. Sai wani haske ya fito min.

Tunda akwai Ajamawa kamar wannan, to Ajami na nan a raye. Mu ne dai ƴan boko da ƴan zamani muke ƙyamar sa. Dalili? Ni a nawa ganin, ba a son Almajirai su fahimci duniyar zamani kada su fara neman cin gumin rayuwar su ma. Mun fi so mu bar su a wanke-wanke, aikace-aikace da kuma leburanci, muna ta bautar da su, da sunan ai mu ƴan takarda ne, mun san abin da duniyar ta ke ci. Wannan ba zata sabu ba, bindiga a ruwa. A lokacin na dawo gadangadan zuwa binciken Ajami.

A take a nan Akwanga, na fitar da tunanin Ajamization of Knowledge. Na dawo Kano, na shiga bincike. Kamar yadda na ce, jagorori na – waɗanda abin ya ba su mamaki ganin yadda na hikikaice – su ne Nasiru Wada Khalil da Fatuhu Mustapha. Sai kuma Muhammad Auwal Ɗankumbotso.

Ba nan ne wurin bayar da sakamakon duk binciken da na yi ba. Amma matakin farko shi ne gabatar da Bakandamiyar Lacca (Inaugural Lecture). Na zama farfesa a 1997, saboda haka na ɗauki kusan shekaru biyar ina nazari kafin in gabatar da laccar a ranar Afrilu 24, 2004. Amma mai ya biyo baya – shiru ka ke ji kamar an aiki bawa garin su!

Gwiwa ta dai ba ta yi sanyi ba. A tsaka-tsakin lokacin daga 2004, ilimi da mallakar kwamfuta ta yawaita. Sai na canza akalar maudu’in – samar da haraffin Ajami a kwamfuta. Ta hanyar samun haruffan boko a ka yawaitar da ilimi a Turai a 1440 wanda Johannes Gutenberg ya yi. A nan, na san akwai haraffun Larabci a kwamfuta, amma duk Hafs ne. Ni, a waje na, rubutun Larabcin Bahaushe Warsu ne. Saboda haka, in dai zaka yi wa Bahaushe rubutu, ya karɓa da hannu biyu, to Warsantar da shi.

A cikin binciken da na yi, na yi karo da Mamoun Sakkal, Balaraben Amurka, kuma mai sana’ar ƙera haruffan kwamfuta (font designer) a Seattle, jihar Washington da ke Amurka. Muka fara magana a kan yadda zai ƙirƙiro min haruffan Warsh na Hausa. Na aika masa da littattafai masu rubutun Warsu daga Kano. Bayan kusan shekaru tara ana ta kai-wa-da-kawowa, ya ce a biya shi $50,000 (dala dubu hamsin). Na ce da shi, “bissalam.” Wane ni?, inji kiyashi a jirgi.

Da Allah (SWT) Ya ga zuciyar ta, da farar niyyar ta, sai kawai Ya kai ni ga wani dandazon Kiristocin SIL International, a Dallas, Texas, Amurka waɗanda suka sadaukar da rayuwar su a kan nemo hanyar da za su Kiristantar da mutane ta hanyar buga Bibul da harsunan mutanen. Hausawa, saboda taurin kan su wajen kafewa akan addinin Musulunci, sai suka zama abin yunƙurawa na farko. SIL suka ɗauki nauyin wata mace mai suna Becca Hirsbrunner Spalinger ta je Jami’ar Reading a Ingila inda ta yi karatun digiri na biyu a fannin MATD (Masters in Art Typeface and Design) a 2015. Project ɗinta shi ne ƙirkiro da harafin Warsu da abin na kira ‘Gardanci’, watau Warsh font. Ta kira shi, Alƙalami. Ta samu samfuran rubutun Gardanci ne daga littaftafan da a ka sayo mata wajen Ajamawan da ke sayar da Littattafai a Kasuwar Kurmi (Kano, Najeriya).

Da ta gama, ta gabatar da shi ga SIL wanda su kuma suka sake shi cikin dajin duniya da niyyar a yi amfani da shi wajen rubuta Bibul da Hausa Warsu. Dalilin yin haka kuwa shi ne la’akari da cewa ba yadda za a yi a sa Hausawa Musulmi su karɓi wani rubutu ba na Ƙur’ani ba, in ba da Warsu aka yi shi ba. Warsu shi ne na su – a duk duniya ba bu wata al’umma da ke da salon rubutun Warsu irin na Hausawa. Pakistan (Urdu), Iran (Farsi), Malaysia (Jawi) da wurare da dama na amfani su ma da Ajami – amma da Hafs. Shi ya sa rubutun Ajamin su ya ke kamar na Larabawa.

Nan da nan na sakko da shi Alkalamin. Na koyawa Abdalla Sani Shu’aibu, hazikin matashi da ke cikin ofishin Visually Ethnographic Networks a Kano. A cikin ƙanƙanin lokacin ya laƙance shi. A karon farko na Ajamanci, sai muka hau juyar da duk wani littafin Hausa da Larabci na tarin Kano zuwa Hausa rubutun Warsu. Waɗannan sun haɗa da Taqyidl Akbar, Kano Ta Dabo Ci Gari, Labarin Tarihin Kano (Kano Chronicle), Waƙar Bagauda, da sauran su. Nan ba da jimawa ba, zan ɗora su duk a Internet domin amfanin kowa, amma duk sadaukarwa ne ga Almajirai. Su san tarihin su.

Ana wannan gaɓar ne, sai Abdullahi Abba Ɗalhatu daga Brazil ya lalubo ni. Ashe ya ga yunƙurin da muke yi, shi ma sai ya bazama. Basirar sa ta fi ta mu, nesa ba kusa ba, domin shi ya iya Larabcin, Ajamancin, sannan kuma maƙirƙirin manhjar kwamfuta ne (programmer). Abin da ya fara yi sai ya kafa ƙungiya Akadamiya. A ƙarƙashin wannan sai ya ɗauko Ƙur’ani fassarar Hausa ta Sheikh Abubakar Gumi ya Ajamantar da fassarar da Hausar Warsu – shafi fiye da 700. Ya yi amfani ne da Harafin Alƙalami da muka kuɓutar da shi daga SIL.

Ganin wannan baiwar ta sa, sai ni da amini na Salisu Ɗanyaro muka ce ya ƙirƙiro mana keken rubutun Ajamin Warsu a wayar hannu, ko nawa ne za mu biya shi. Wannan ma sadaukarwa ce ga Almajirai, saboda su samu hanyar isar da saƙonni ga ƴan uwan su, abokai da iyayen su. A yanzu dai Abdullahi na kan yin hakan.

Bayan wannan, akwai sanannen littafi Mu Koyi Ajami da Larabci na Na’ibi Suleiman Wali da Halliru Binji wanda Gaskiya Corporation Zariya suka buga. Shi ma ni da Abdalla Sani Shuaibu mun surantar da shi da Alkalami font saboda zamanantar da shi. To amma matsalar ita ce samun iznin acibilistar da shi ga jama’a, wanda sai da iznin masu kamfanin. Mun fara tuntubar su, amma ba mu kai ga ko’ina ba. Kwatsam sai Abdullahi ya rubuta nasa littafin mai suna “Koyon Ajami da Boko”. Kuma ya ce kyauta ne ga duk al-acibilisti. Nan da da jimawa ba za a saka shi inda kowa zai samu.

Ana cikin jira sai ya ƙirƙiro da wata dabara ta juya Hausar boko zuwa Hausar Ajami Warsu ta hanyar gidan yana a intanet. Za ka rubuta sakon ka da Hausar boko, manhajar sai ta Ajamantar da shi. Abin gwanin ban sha’awa. Yi tunanin mutumin da ya iya boko, amma zai aika sako ga wanda bai iya ba. Wannan hanyar — ta farko a adabin Hausa — ita ce hanyar muhawara mai sauki a gare su! Waya dai ta zama ruwan dare yanzu – har Almajirai ma na da ita!  A yanzu shima wannan yana kan gwaji. Da zarar duk mun kammala komai da komai, za a sanar. Ga dai hoton misali na maƙala a ƙarshen wannan dogon rubutun!

Ajamanci shi ne kaɗai hanyar da za mu yi amfani da ita wajen wayar da kan mutanen mu da ake iƙirarin jahilai ne saboda ba su san boko ba. Yaya za ka ce kana koyar da yaƙi da jahilci ga mutumin da ke hanyar zama farfesa, kawai saboda ba salon rubutun ku ɗaya ba, kuma ba ka da niyyar bin nasa salon don ilmintar da shi, sai naka domin daɗa duhuntar da kuma daƙile shi?

A duk wannan yunƙurin tun daga 1996 har yanzu, ban nemi tallafin gwamnati ba. Kuma bana nema. Amma mai gwamnati za ta yi ta faranta min? Misali, duk rubutacciyar sanarwa a Asibitoci ko kasuwanni, a yi du da Ajami. Ko Turawan mulkin mallaka sun girmama wannan basirar – sunayen Unguwannin mu a Kano duk da Ajami aka rubuta su. Mace ta zo antenatal ga fastoci na wayar wa, amma duk da boko, kuma ba ta iya bokon ba. Yi su da Ajami ka sha mamaki.

Duk sunayen ofisoshin gwamnati a suranta su da Ajamin Warsu. Ban ce a cire bokon ba, amma a gefe, ko kuma ƙasa, a suranta su da Ajami. Haka a ke yi a Ethiopia da Amharic. Sunayen manyan tituna da sunayen garuruwan da ke ƙarkashin mallakar Kano, a rubuta su da Ajami.

Mai kuma jama’ar gari za su yi? Duk mai shago, ko supermarket, ko Plaza, ko Mall, kuma mai kishi, ya rubuta sunan wurin da Ajamin Warsu. Duk wani katin sanar da daurin aure, a yi shi da Ajamin Warsu. In an yi haka, an biya ni.

Illus.

232 thoughts on “Ajami a Sauƙaƙe, daga Abdalla Uba Adamu

  1. купить диплом врача с занесением в реестр [url=https://prema-diploms.ru/]купить диплом врача с занесением в реестр[/url] .

Comments are closed.