January 15, 2025

Ambaliyar ruwa ta tilasta wa dalibai daina zuwa makaranta a Bauchi

0
IMG-20240702-WA0029.webp


Daga Sabiu Abdullahi
  
Wata mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a garin Dambam hedikwatar karamar hukumar Dambam a jihar Bauchi, ta mamaye makarantar firamare ta Model Central, lamarin da ya tilastawa daliban zama a gida.

An rawaito cewa an tilasta wa daliban dakatar da zuwa makaranta na wani dan lokaci har sai yankin ya bushe, wanda hakan na iya haifar da asarar tsawon zangon karatu gaba daya.

Wani mazaunin garin da ya yi magana da ƴan jarida ta wayar tarho wanda ba a bayyana sunansa ba, ya ce an shafe shekaru ana fama da matsalar, inda gwamnati ta kasa daukar kwararan matakai.

A cewarsa, “Wannan lamari ne da ke faruwa a duk lokacin damina,” inda ya ce idan irin haka ta faru, dole ne yaran su daina zuwa makaranta har na tsawon watanni uku har sai an daina damina.
Ya bayyana takaicin yadda gwamnati ta yi watsi da makarantar, tare da hana yara samun ilimin asali.

Ya kuma bukaci gwamnatocin kananan hukumomi da jihohi da su shawo kan lamarin domin tabbatar da cewa yara sun samu ilimi wanda shi ne babban hakkinsu.

Da take mayar da martani kan lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho, kwamishiniyar ilimi ta jihar Dr. Jamila Dahiru ta ce gwamnati na kan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *