Peter Obi ya ziyarci Sule Lamido a Abuja
Daga Abdullahi I. Adam
Tsohon gwamnan Anambra Peter Obi ya ziyarci Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa, a Abuja
Hadimin tsohon gwamnan jihar Jigawa kan lamuran sadarwa, Mal. Mansur Ahmed, ne ya bayyana cewa a yau Litini ne Peter Obi ya ziyarci maigidan nasa a babban birnin tarayya, Abuja.
Mal. Mansur ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa “ɗan takarar shugaban Ƙasa a Jam’iyyar Labour Party a 2023, Peter Obi ya ziyarci Jagoran talakawa Dr. Sule Lamido CON, a gidansa da ke Abuja.”
Irin wannan ziyara ka iya zama wani mataki ne na shiri da ‘yan siyasar ke yi don shirin kakar zaɓe mai gabatowa a shekarar 2027 don cigaba da damawa a fagen siyasar na Nigeria.