Jerangiyar Google Pixel 9: Sabon salo a duniyar wayoyin salula

Daga Sabiu Abdullahi
Google ya ƙaddamar da sabbin wayoyi na Google Pixel 9, waɗanda suka haɗa Google Pixel 9, Google Pixel 9 Pro, Google Pixel 9 Pro XL, da kuma Google Pixel 9 Fold.

Waɗannan wayoyi suna dauke da sabbin fasahohi da ingantattun abubuwa, kuma suna da ingantaccen tsarin hotuna wanda ya hada da kyamarori masu karfin gaske.
Kyamarar baya tana daukar hoto da sauri da kuma inganci, yayin da kyamarar gaba ta kara inganta wajen daukar hoton fuska da bidiyo.
Google Pixel 9 na amfani da sabon tsarin aiki na Android wanda ya zo da sabbin fasahohi na tsaro da kuma ingantaccen aiki.
Wayar tana da kyakkyawan sikirin ƙirar OLED wanda ke bayar da haske da kuma launuka masu kyau, wanda hakan zai ba ka damar jin dadin kallo da kuma buga gyam.
Bugu da kari, Google Pixel 9 suna dauke da sabbin na’urorin hade da kwamfutar hannu da suke aiki tare don gamsar da kwastoma. Wannan sabuwar waya tana da babban batir da zai iya dorewa na tsawon lokaci, wanda ke nufin cewa za ka iya amfani da wayar ka tsawon rana ba tare da damuwa ba.

Wani abu kuma da masu sharhi suka ambata shi ne dangun wayar ya yi kama da na wayoyin iPhone na zamana
A takaice, Google Pixel 9 suna da kyan gani da za su faranta wa masu amfani rai, tare da inganta yanayin amfani da wayar.
