Shugaba Tinubu Ya Sauke Shugabar Jami’ar Abuja

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sauke Farfesa Aisha Maikudi daga mukaminta na shugabar Jami’ar Abuja, wacce aka fi sani da Jami’ar Yakubu Gowon.
Sanarwar da kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis, ta bayyana cewa an maye gurbinta da Farfesa Lar Patricia Manko a matsayin shugabar riƙo na wata shida. Sai dai sanarwar ta ce ba za ta iya neman mukamin shugabar dindindin ba idan lokacin ya yi.
Farfesa Aisha Maikudi an naɗa ta a watan Yuni 2024 bayan cikar wa’adin mulkin tsohon shugaban jami’ar, Farfesa Abdulrasheed Na’Allah. Naɗinta ya haifar da ce-ce-ku-ce, inda wasu ke ganin ba ta cancanta da mukamin ba.
Kazalika, Shugaba Tinubu ya naɗa Sanata Lanre Tejuoso a matsayin sabon shugaban gudanarwar jami’ar (Pro Chancellor). Haka kuma ya sauke shugaban Jami’ar Nsukka, Farfesa Polycarp Emeka Chigbu, inda ya naɗa Farfesa Oguejiofu T. Ujam a matsayin shugabar riƙo na tsawon wata shida.