October 18, 2025

Zulum ya raba gidaje tare da yin alkawarin tallafa wa ƴan gudun hijira

FB_IMG_1708876668769.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya raba wa ‘yan gudun hijira gidaje 447 a ranar Lahadi a yankin Dalori da ke karamar hukumar Konduga.



Mutanen da suka ci gajiyar tallafin, wadanda kuma rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu, sun samu muhimmin tallafi domin su koma matsagunansu.

Zulum ya ce gwamnati ta ba su tallafin jin kan ne don komawa gida su zama masu dogaro da kansu.

Magidanta 447, wadanda suka kunshi kusan iyalai 2,500, an fito da su ne daga sansanonin ‘yan gudun hijira guda biyu: 197 daga Kawar Maila da 250 daga garin Dalori.

Kowane gida ya sami kayan abinci, tabarma, barguna, da kayan sawa.

Gwamna Zulum ya bayyana mahimmancin samar da rayuwa mai dorewa ga al’ummomin da suka koma gudun hijira.

2 thoughts on “Zulum ya raba gidaje tare da yin alkawarin tallafa wa ƴan gudun hijira

  1. Heya i am for tthe first time here. I caame acrss this board and I fond
    It treuly usseful & itt helped mee out a lot. I ope
    to give something back andd aid others luke you helped me.

Comments are closed.