January 14, 2025

BH ta kai hari kan ayarin motocin Gwamna Mai Mala Buni

9

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, a yammacin ranar Asabar, ya tsallake rijiya da baya, yayin da wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun yi wa ayarin motocinsa kwanton bauna, inda suka kashe dan sanda guda tare da raunata wasu 6 a hanyar Jakana zuwa Mainok a jihar Borno.

Tawagar jami’an tsaron dai tana cikin ayarin motocin da suka raka gwamnan jihar Maiduguri domin gudanar da taro a Jami’ar Maiduguri, inda aka baiwa mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima digirin girmamawa.

Sai dai kuma ‘yan ta’addan ba su sani ba, bayan taron, tawagar jami’an tsaron ta koma Yobe, amma ba tare da gwamnan ba, wanda ya tsaya a Maiduguri yana shirye-shiryen wata tafiya zuwa Abuja domin wata ganawa.

9 thoughts on “BH ta kai hari kan ayarin motocin Gwamna Mai Mala Buni

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *