January 15, 2025

Wani mutum ya mutu a rijiya yayin ceto dansa da ya zame a ciki

0
kano-well-750x475.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Wani mutum ɗan shekara 49 mai suna Fasasi Afees a ranar Alhamis ya nutse a cikin wata rijiyar a cikin gida a lokacin da yake kokarin ceto dansa Kaleed mai shekaru 17 da haihuwa.

Lamarin dai ya faru ne a Gaa Jangbo da ke karamar hukumar Offa a jihar Kwara. 

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Hassan Adekunle ya ce jami’an kashe gobara sun samu nasarar ceto Kaleed tare da samo gawar mahaifin nasa.

“Mun gano mahaifin da ya mutu yayin da muka iya ceto yaron da ransa a kauyen New Maselu, Offa,” in ji Adekunle.

Rahoton ya ce yaron ya je diban ruwa ne a rijiyar, kawai sai ya zame.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *