Za a fara samar da aikin yi ga waɗanda suka gama NYSC—Majalisa

Shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin matasa da zamantakewar al’umma, Yemi Adaramodu (mai wakiltar Ekiti ta Kudu) ya bayyana cewa kudurin dokar asusun tallafawa matasa masu yi wa kasa hidima, kwanan nan zai samar da ayyukan yi ga wadanda suka kammala karatu.
Adaramodu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci wata tawagar kwamitin ziyarar wani aiki da suka kai sansanin masu yi wa kasa hidima na NYSC da ke Iseyin a jiya Asabar.
Ya ce, kudirin dokar, ya wuce karatu na farko dana biyu, da sauran muhimman dokoki, nan ba da jimawa ba za a aika wa shugaban kasa don amincewa.
Dan majalisar ya kuma bayyana cewa, za’a samar da wannan kudiri ne don tabbatar da cewa mambobin kungiyar sun samu damar tsayawa da kafafunsu bayan sun kammala bautar kasa, ta hanyar horaswar da ake samu daga shirin NYSC Skill Acquisition and Entrepreneurship, SAED,.
Ya kara da cewa tanade-tanaden daftarin dokar ya kuma shafi ’yan kungiyar da ke son shiga kasuwanci bayan shekarar hidimarsu.