January 13, 2025

Majalisa za ta binciki yadda manyan makarantun Najeriya ke ba da gurbin karatu bisa ka’ida ba

0
IMG-20231109-WA0003.jpg

Daga Usama Taheer Maheer

Majalisar dattijai za ta yi bincike akan yadda makarantun gaba da sakandare ke bayar da gurbin karatu ba bisa ka’ida ba.

Majalisar Dattijai ta umarci kwamitinta na ɓangaren makarantun gaba da sakandare da kwamitin karɓar ƙorafe-ƙorafen al’umma, da su yi binciken a kan zargin da ake yi wa makarantun gaba da sakandare a kan bayar da da gurbin karatu ga waɗanda ba su cancanta ba.
Ana sa ran kwamitocin za su sanya hukumar JAMB a cikin binciken nasu.

Ana sa ran kwamitocin za su sanya hukumar JAMB a cikin binciken nasu.

Da yawan ƙorafe-ƙorafe na nuna cewa, jami’o’i da kwalejoji suna haɗa baki da hukumar JAMB wajen ba wa waɗanda basu cacanta ba gurbin karatu.

Tun da fari, ɗan majalisar da ke wakiltar Ebonyi ta arewa, Mista Nwebonyi Onyeka, shi ya karanta ƙudirin a gaban majalisar. Yayin da ya samu goyon bayan ƴan majlissu da dama.

Yayin Jawabin ɗan majalisar, ya yi zargin cewa, ana samun haɗin gwiwa da hukumomin makarantun gaba da sakandare da hukumar JAMB wajen samar wa da ɗalibai gurbin karatu ba bisa ƙa’ida ba.

Ɗan majalisar ya ƙara da cewa, yawanci ana karɓar kuɗin ɗaliban da ke neman kwasa-kwasan da ke da wahalar samu, kamar karatun likitanci, karatun sarrafa magunguna, karatun shari’a, da karatun injiniyarin har ma da karatun masu jinya a sibiti.

Ya kuma yi zargin cewa, da yawan ɗaliban da suke da hazaƙa, sun shiga damuwa, wasu ma sha’awar karatun ya fita daga ransu saboda wannan rashin adalcin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *