Majalisa ta ba da umurnin duba lamarin albashin malaman jami’o’i
Daga Usama Taheer Maheer
Shugaban majalisar wakilai Tajuddin Abbas ya ba wa kwamitocin majalisar mako biyu domin kawo mafita a kan batun albashin wata takwas da aka riƙewa malaman jami’a.
Kwamitocin da aka ba wa umarnin sun haɗa da kwamitin ilimin jami’o’i, kwamitin kuɗi, kwamitin kula da haƙƙuna, kwamitin kula da ma’aikata da kwamitin sharia na majalisar.
Tunda farko dai ɗan majalissa Poul Nnamchi mai wakiltar Enugu da haɗin gwiwar ɗan majalisar da ke wakiltar Zamfara, Aminu jaji da Julius Ihonvbere mai wakiltar Edo, sai Lilian Orogbu daga Anambara su ne suka gabatar da ƙudirin a gaban majalisar.
Nnamchi ya bayyana muhimmancin malaman Jami’o’i wajen taimaka wa harkan ilimi, ta hanyar koyarwa da kuma sanya shugabannin gobe a bigere na gaskiya.
Ɗan Majilisar ya bayyana yanda riƙe albashin ya shafi walwalar malaman da kuma yanda ya ƙara gurgunta harkar koyo da koyarwa a matakin jami’o’i a ƙasar.