October 18, 2025

Sevilla FC ta Laliga ta aika da saƙon ta’aziyya kan ibtila’in gobarar tankar mai a Jigawa

image_editor_output_image-1913662317-1729227865594.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Bayan mummunan gobarar tankar fetur da ta faru a Majia, karamar hukumar Taura ta jihar Jigawa, wadda ta halaka daruruwan mutane tare da jikkata wasu da dama, kungiyar kwallon kafa ta La Liga, Sevilla FC, ta miƙa ta’aziyyarta ga wadanda lamarin ya shafa.

A wata wallafa da kungiyar ta yi a shafinta na Facebook ranar Alhamis, kungiyar kwallon kafar ta bayyana jimaminta game da wannan masifa.

Sun ce, “Muna tura addu’o’i tare da tunani ga dukkan wadanda bala’in Jigawa ya shafa a Najeriya a wannan mawuyacin lokaci.”

Sakon ya haɗa da tutar Najeriya, wanda ke nuna haɗin kai da goyon bayan da kungiyar ke bayarwa ga al’ummar Najeriya a wannan yanayin na bakin ciki.

Wannan mummunan al’amari da ya faru a farkon makon nan ya jefa mutane cikin tashin hankali a fadin kasar, yayin da ake ci gaba da ɗaukar matakai don tallafa wa waɗanda suka tsira da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

Hukumomi na ci gaba da bincike game da musabbabin wannan hadari yayin da al’umma ke ci gaba da jimamin asarar rayuka.

7 thoughts on “Sevilla FC ta Laliga ta aika da saƙon ta’aziyya kan ibtila’in gobarar tankar mai a Jigawa

  1. Hey I know this iis off topic bbut I was wonderring if yyou kmew off anny widgets I coukd
    add too my blog that autmatically tweeet my
    newest twutter updates. I’ve been looking ffor a plug-in like this for quitee some tim
    annd wwas hopiing maybe yyou would havee somke experience with something like
    this. Plase leet mee kow if you run into anything.
    I truy enjiy reading youir bpog and I look forward to
    your neew updates.

Comments are closed.