Shin kuna da labarin arzikin Dangote ya nunku zuwa $28bn bayan matatar mansa ta fara aiki a watannin baya?
Daga Sabiu Abdullahi
Alhaji Aliko Dangote, attajirin Najeriya kuma Babban Shugaban Kamfanin Dangote Refinery, ya ci nasarar riɓanya arzikinsa zuwa dala biliyan 28 bayan matatar mansa ta fara aiki.
A cewar rahoton Bloomberg Billionaires Index na ranar Alhamis, fara aikin matatar man da ake ta tsammani a Najeriya ya kara wa Dangote makudan kudade, wanda ya sa ya ninka dukiyarsa sosai.
Matatar Dangote tana cikin yankin kasuwanci na Lekki a Ibeju-Lekki, jihar Legas, kuma ita ce mafi girma a duniya ta fuskar tsarin aiki guda (single-train oil refinery), tare da kasancewa cikin mafi ci gaba, inda take da damar tace dukkan nau’ikan man fetur na duniya.
“Matatar tana da damar sauya tattalin arzikin Najeriya ta hanyar samar da isasshen mai a cikin gida. Haka kuma ta ninka dukiyarsa zuwa dala biliyan 27.8,” in ji Bloomberg.
Ana sa ran matatar za ta canza yanayin bangaren makamashi a Najeriya, inda za ta fara samar da kayayyakin mai a cikin gida, wanda hakan zai iya kawo karshen dogaro da shigo da mai daga kasashen waje.
Masana sun yi hasashen cewa arzikin Dangote zai iya ci gaba da bunkasa a watannin da ke tafe.
Yayin da matatar ke kara samar da kayayyakin mai da fadada aikinta, Dangote na shirin mamaye kasuwar man fetur ta Najeriya, inda yake da shirin fitar da wasu kayayyakin zuwa kasashen Afirka.
A shekarunsa na 67, Dangote ya gina mafi yawan dukiyarsa ta hanyar mallakar kashi 86 cikin 100 na hannun jari a kamfanin Dangote Cement, wanda kimarsa ta kai fiye da dala biliyan 9, tare da ayyukansa a kasashe goma na Afirka.
Baya ga siminti, Dangote Group na da hannun jari a bangarori kamar samar da abinci, taki, da gidaje.