January 15, 2025

Hadarin mota ya yi ajalin mutane 11 a Jigawa

14
ACCIDENT-SCENE.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Wani mummunan hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 11 a garin Kwanar Gujungu da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da faruwar hatsarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Hadarin dai ya afku ne da misalin karfe 12:00 na dare inda motocin biyu suka yi karo da juna, inda nan take aka samu asarar rayuka.

Motar kirar Honda mai dauke da fasinjoji biyar da direba Abdullahi Muhammad, ta yi karo da motar Golf wadda ke dauke da fasinjoji hudu da direban mai suna Safiyanu Mamu.

14 thoughts on “Hadarin mota ya yi ajalin mutane 11 a Jigawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *