October 18, 2025

Isra’ila ta hallaka ‘yan ƙasarta 13 da aka yi garkuwa da su a Gaza

FB_IMG_1696883405801.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Jiragen yaƙin Isra’ila sun hallaka Isra’ilawa da ‘yan kasashen waje akalla 13 da aka yi garkuwa da su a arewacin Gaza a cikin awa 24 da suka gabata.

Wannan sanarwar ta fito ne daga reshen mayakan kungiyar Hamas.

A cewar Qassam Brigades a wata sanarwa da ta fitar, jiragen yakin Isra’ila sun hallaka “fursunoni goma sha uku.. ciki har da ‘yan kasashen waje” a wurare biyar da suka kai hari

Isra’ila ta ɗauki aƙalla mako guda tana luguden wuta a yankin Gaza da ta mamaye — inda kimanin mutum miliyan 2.4 suke zaune cikin matsatsi.

Baya ga haka, ta rusa gine-gine sannan ta kashe fiye da mutum 1,500.

Isra’ila ta ce Hamas ta yi garkuwa da fiye da mutum 150, da suka hada da fararen-hula da jami’an tsaron kasarta.

2 thoughts on “Isra’ila ta hallaka ‘yan ƙasarta 13 da aka yi garkuwa da su a Gaza

  1. Ищете качественного сантехника в Минске? Мы предлагаем полный спектр услуг с гарантией надежности. Наши квалифицированные сантехники готовы провести чистку. Узнайте больше на установка унитаза минск.

Comments are closed.