January 15, 2025

Amurka ta ce Isra’ila ta amince da tsagaita wuta na sa’o’i 4 duk rana saboda fararen hula su tsere

0
FB_IMG_1698036566675.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Isra’ila ta amince da tsagaita wuta na tsawon sa’o’i hudu a kullum a arewacin Gaza domin barin fararen hula su gudu, fadar White House ta fada jiya Alhamis.

Biden dai ya dade yana matsawa Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu lamba don tsagaita bude wuta a yakin da aka shafe fiye da wata guda ana gwabzawa.

Sojojin Isra’ila da na Hamas na ci gaba da gwabza kazamin fada a garin Gaza da ke arewacin zirin Gaza.

Kakakin kwamitin tsaron kasar John Kirby ya shaida wa manema labarai cewa, “Isra’ila za ta fara tsagaita wuta na sa’o’i hudu a yankunan arewacin Gaza a kowace rana, tare da bayar da sanarwar sa’o’i uku kafin nan.”

“Isra’ilawa sun gaya mana cewa ba za a yi wani aikin soji ba a wadannan yankuna na tsawon lokacin da aka dakatar (kuma) wannan tsari zai fara ne a yau.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *