Harin da aka kai kan motocin daukar marasa lafiya a Gaza ya yi sanadiyyar rasa rayuka 15
Daga Sabiu Abdullahi
Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta sanar da cewa mutane 15 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da Isra’ila ta kai kan motocin ɗaukar marasa lafiya a kusa da asibitin Al-Shifa da ke Gaza.
Lamarin ya faru ne a hanyar da aka yi niyyar jigilar marasa lafiya daga Gaza ta mashigar Rafah.
Hukumar ta PRCS ta bayyana cewa tawagar da ke kan hanyar zuwa Asibitin Al-Shifa mai nisan kilomita daya kacal, wasu mahara ne suka kai musu hari har sau biyu.
Motocin, dauke da marasa lafiya a cikin mawuyacin hali, an buge su ne duk da cewa sun nuna matsayinsu a matsayin motocin daukar marasa lafiya.
A cewar PRCS, tun farko motocin daukar marasa lafiya suna jigilar marasa lafiya daga Asibitin Al-Shifa don saukaka kwashe su daga Gaza.
Sai dai bayan tafiyar kilomita hudu daga asibitin, ayarin motocin sun gano an tare hanyar, lamarin da ya tilasta musu komawa baya. An kai wa motocin hari ne a yayin da suke komawa, lamarin da ya janyo hasarar rayuka da dama.
Rahotannin farko da aka samu daga ma’aikatar lafiya ta Hamas a Gaza na nuna cewa aƙalla mutane 13 ne suka mutu sakamakon fashewar wani bam a wajen asibitin Al-Shifa.
Sashen bin diddigi na BBC ya tabbatar da sahihancin bidiyo da hotuna da ke nuna waɗanda suka jikkata da waɗanda suka mutu a kwance a wajen harabar asibitin.
A wani yanayi na daban, sojojin Isra’ila sun mayar da martani ga wannan zargi, inda suka ce wadanda suka mutu a harin mayakan Hamas ne.
Sojojin Isra’ila sun yi zargin cewa Hamas na amfani da motocin daukar marasa lafiya wajen jigilar mayaka da makamai. Sai dai har yanzu ba su bayyana wata kwakkwarar shaida da ke goyon bayan ikirarin nasu ba.