Gwamnatin Jigawa Ta Dakatar Da Ma’aikata Kan Zargin Karkatar Da Sama Da Naira Biliyan 1.7

Daga Sabiu Abdullahi
An dakatar da jami’an da ke da alhakin aiwatar da shirin farfado da tattalin arziki na naira biliyan 1.7 na COVID-19 a jihar Jigawa sakamakon zarge-zargen almundahana.
Shirin an yi shi ne don tallafa wa ƙungiyoyi masu rauni da annobar ta shafa, waɗanda suka haɗa da manoma da ƙananan ‘yan kasuwa.
Sakamakon binciken da aka aiwatar ya nuna jami’an ofishin Fadama III na jihar, sun bayar da naira 8,000 ne kacal ga manoma maimakon N150,000 da aka ware wa kasafin kudin da kayayyakin noma.
Majalisar zartarwar jihar ta amince da dakatar da kodinetan jihar da jami’an 27 nan take, har sai an ci gaba da nazari da kuma daukar mataki.