Lalacewar naira ta kai ana sayar da dala 1 a kan naira 1355
Daga Sabiu Abdullahi
Har yanzu dai abubuwan sun ƙi yin kyau a yayin da kudin Najeriya (naira ) ke ci gaba da faduwa a kan dalar Amurka, inda ake sayar da dala ɗaya a kan N1,355 a kasuwar bayan fage tun a ranar Alhamis.
Wannan na zuwa ne watanni biyar bayan da dala ta fara haye N1,000 a kasuwar bayan fagen.
Rashin darajar naira na ci gaba da haddasa mummunar tsadar rayuwa ga ‘yan Najeriya.