October 18, 2025

Gwamnan Katsina ya naɗa tsohon soja Ahmad Daku a matsayin shugaban Hibah

image_editor_output_image-748463056-1702489152158.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Gwamna Dikko Radda na Katsina ya amince da nadin tsohon gwamnan mulkin soja na jihohin Kano da Sokoto, Birgediya-Janar Ahmad Daku a matsayin Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar.

Gwamnan ya kuma nada Dokta Ahmad Filin-Samji a matsayin Shugaban Hukumar Zakka da Wakafi mai kula da harkokin sadaka da bayar da tallafi da kuma harkokin kawance.

Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Ibrahim Kaula ne ya sanar da nadin a ranar Laraba a Katsina.

Daku ya rike mukamin Gwamnan Soja na Jihar Kano daga 1985 zuwa 1987, sannan kuma Jihar Sakkwato daga 1987 zuwa 1990, sannan a shekarar 2002, ya zama Gwamnan Jihar Kano.

Ya kuma jagoranci Hukumar Kula da Alhazai.

A cewar Kaula, Sheikh Aminu Abu-Amar zai kasance kwamandan Hisbah na jiha, tare da Sheikh Kamal Alti, Malam Iliya Imam da Malam Sirajo Lawal-Katsayal a matsayin mambobin hukumar.