November 8, 2025

Wata budurwa ta kashe kanta saboda mutuwar saurayinta

IMG-20231126-WA0026.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Wata ma’aikaciyar lafiya mai suna Florence Vandi ‘yar shekara 22 a cibiyar kula da lafiya matakin farko a karamar hukumar Girei a jihar Adamawa, ta kashe kanta bayan mutuwar saurayinta.

Rahotanni sun nuna cewa ta sha wani sinadari ne wanda ke iya halaka mutum.

Lamarin dai ya faru ne a ranar 12 ga watan Disamba, 2023, sa’o’i kadan bayan rasuwar saurayinta, Nuhu Boniface.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya fitar da wata sanarwa inda ya tabbatar da faruwar lamarin.

Nguroje ya ce, “Bincike ya kara nuna cewa har zuwa rasuwarta, Florence ma’aikaciyar lafiya ce a cibiyar kula da lafiya a matakin farko ta Girei.”

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Afolabi Babatola, ya bayyana matukar bakin cikinsa kan lamarin, inda ya bukaci jama’a da su guji daukar al’amura a hannunsu, kuma su gaggauta kai rahoton duk wani abu da ya shafi ‘yan sanda.