December 7, 2025

An aike da yan ta’adda sama da sittin barzahu a Sokoto

IMG-20231025-WA0026.jpg

Daga Bello Badamasi Dinawa

A jiya Talata, Rundunar Sojojin Najeriya ta ce ta samu nasarar hallaka ‘yan Bindiga da dama tare da kwato makamansu a kauyen Tukandu dake Gundumar Sakkwai a karamar Hukumar Tangaza dake jahar Sokoto.

Kamar yadda kakakin rundunar Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya bayyana a shafinsu yace, da yammacin jiya Talata ne dakarunsu su ka fafata da ƴan-ta’addan.

Ana zargin ɓarayin sun zo kauyen da nufin ramuwar gayya kan hallaka wasunsu da aka yi a yankin Kwanuka kalilan da su ka gabata, sai dai kuma ko yanzu basu sha da daɗi ba.

An samo Bindigu kirar AK-47 guda Ukku da wata Bindiga ta musamman kirar PKT, hadi da Alburusai 125 masu tsawon Mita 7.62Mm bayan da an kashe wasun su da yawa.

Wasu daga cikin makaman da aka kama

17 thoughts on “An aike da yan ta’adda sama da sittin barzahu a Sokoto

Comments are closed.