Gwamna Fintiri ya yi wa ƴan bautar ƙasa ƙarin ‘alawi’ na N10,000

Daga Sabiu Abdullahi
Gwamna Ahmadu Fintiri ya bayyana a ranar Talata cewa masu yi wa ƙasa hidima (watau NYSC) da ke aiki a jihar Adamawa za su riƙa samun ƙarin alawus na naira 10,000 duk wata daga watan Janairun shekara mai zuwa a ƙoƙarin rage raɗaɗin matsalar cire tallafin man fetur.
Gwamna Fintiri ya bayyana hakan ne a yayin bikin rantsar da rukunin C Ɓangare na 2, inda aka tura ƴan bautar ƙasar 1,340 zuwa jihar.
Wannan ƙarin alawus ɗin dai zai fara zuwa ne baya ga kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke bayarwa ta tsarin masu yi wa kasa hidima (NYSC) da kuma ƙari na naira 20,000 da gwamnatin jihar ke bayarwa bayan kammala shekarar hidimar.
Gwamnan ya bayyana cewa wannan shiri na daga cikin ƙudirin gwamnatinsa na tallafa wa matasa a lokutan sauyin tattalin arziki, kamar cire tallafin man fetur.
A jawabin da ya yi wa ’yan bautar ƙasar, ya buƙace su da su ɗauki matakin tura su da sanin makamar aiki a matsayin wata dama ta ganowa da kuma amfani da basirarsu.