Ambaliya Ta Hallaka Mutum 21 a Neja, Ta Lalata Gidaje Fiye da 50

Hukumomin jihar Neja sun tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 21 sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta auku a ƙaramar hukumar Mokwa da ke arewacin Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa akwai mutane 10 da har yanzu ba a gano inda suke ba, lamarin da ke kara tayar da hankali a yankin.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, Ibrahim Hussaini, ya bayyana cewa ambaliyar ta lalata gidaje sama da 50 a ƙauyukan Tiffin Maza da Anguwan Hausawa, bayan ruwan sama mai ƙarfi da ya shafe sa’o’i yana zuba.
Yanzu haka jami’an ceto na ci gaba da aikin neman mutanen da ruwa ya rutsa da su, inda ake fatan samun ragowar da suka bace da rai.
Wani mazaunin yankin da ya shaida lamarin ya ce ambaliyar ta auku ne cikin dare, bayan wata guguwa da ta haddasa mamakon ruwa da ya mamaye unguwanni.