Kotu ta yanke wa Murja Kunya hukuncin zaman gidan yari
Wata babbar kotu da ke Kano ta yanke wa fitacciyar ‘yar TikTok, Murja Kunya, hukunci bayan ta bayyana a cikin wani bidiyo tana zubar da takardun naira, abin da ke keta doka.
Sai dai kotun ta ba ta zaɓi, inda ta ce Murja za ta iya biyan tarar naira 50,000 maimakon zaman gidan gyaran hali.
A wani mataki na daban, Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta bayyana Murja a matsayin jakadiyya tare da haɗin gwiwar Babban Bankin Najeriya (CBN), domin wayar da kan jama’a game da illar raina ko lalata takardun kuɗi.

